Yadda tsadar kula da motar hawan mutum kan sa ya yar da ita a gefen titi saboda ba zai iya kula da ita ba.
Idan kana da mota a Ingila, wajibi ne ka biya mata inshora, da harajin mota (tax) ko kuma takardar gwajin inganci (MOT) domin ta yi yawo a bisa titi. Haka kuma kudin gyaran mota, idan ta lalace, ba kadan ba ne. Sannan ga kudin petir!
Idan aka hada wadannan kudade, yakan fi karfin wasu mutane da albashin su ba shi da yawa. Sai su ga gara su yi amfani da kudin wajen abubuwan da aka fi bukata na rayuwa – kamar abinci, kudin haya da sufurin bus ko jirgin kasa dan zuwa aiki.
A irin wannan yanayi ne masu motoci kan ga cewa ya fi musu sauki yi su yi watsi da motar a gefen hanya, maimakon su biya kudaden da na lissafa.
Karanta Karin Wani Labarin: Yadda aka yi jigilar Uranium a asirce daga Venezuela zuwa Amurka
An kiyasta cewa sama da motoci 21,000 aka yi watsi da su a Birtaniya a shekarar 2021.
Yin watsi da mota laifi ne a karkashin dokar Refuse Disposal (Amenity) Act 1978. Idan aka gurfanar da mutum a kotu kuma aka same shi da laifi, zai iya fuskantar tarar kudi har fam £2,500, kimanin Naira miliyan hudu da dubu dari takwas.




Jamilah Tangaza
