Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kara albashin alkalai da ninki uku
Hausa

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kara albashin alkalai da ninki uku

Tinubu, CEOs, Nigeria,uku

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu kan dokar kara albashin alkalai da ninki uku.

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harokin Majalisa Basheer Lado, ya bayyana cewa a ranar Talata shugaban kasar ya sanya hannu kan dokar karin albashi alkalai da kashi 300%

Karin Wani Labarin: Ƴan mata uku sun mutu a ruwa yayin zuwa yanko ciyawa a Jigawa

A watan Jun ne Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da kudurin dokarin karin albashin alkalai da kashi 300%, wanda shugaban kasa ya aike mata.

Sanata Lado ya bayyana rattaba hannu kan kudirin da shugaban kasar ya yi a matsayin wani gagarumin nasara da kuma ke nuna jajircewarsa wajen kyautata rayuwar ma’aikatan Najeriya.

Lado ya kuma bukaci alkalai a kasar da su kara himma wajen ganin an tabbatar da adalci da kuma gaggawa.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *