Wata ’yar kasuwa a Jihar Gombe, ta tsallake rijiya da baya, biyo bayan hari da ake zargin saurayinta ya kai mata da guduma har cikin gidanta tare da yunƙurin kashe ta.
Lamarin ya faru ne a unguwar Pantami da ke birnin Gombe, inda matar ta samu munanan raunuka amma ta tsira bayan ihun neman ɗauki da ta yi.
Ihun da ta yi ya jawo hankalin maƙwabta inda suka yi ƙoƙarin kawo mata agaji.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce ta kama wanda ake zargi, Musa Adamu mai shekaru 35, mazaunin unguwar Riyal, bisa zargin yunƙurin kisa, fashi da makami, da kuma jikkata mutum.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce wanda ake zargin ya tsallaka katangar gidan matar ne da misalin ƙarfe 2 na dare sannan ya shiga ɗakinta ba tare da izini ba.
Bayan shigarsa, an ce ya doka mata guduma ta ƙarfe, sannan ya yi ƙoƙarin shaƙe ta da igiyar USB kafin ya kwashe kuɗi har Naira 100,000.
Sai dai matar ta samu damar yin ihu, abin da ya sa maharin ya tsere kafin daga bisani a cafke shi.
Bayan faruwar lamarin, ’yan sanda sun garzaya da matar asibiti, inda likitoci suka ba ta kulawa, daga baya kuma aka sallame ta bayan ta samu sauƙi.
Binciken ’yan sanda ya nuna cewa wanda ake zargin ya taɓa neman matar ta ba shi kuɗi, amma ta ƙi amincewa da buƙatarsa.
Karnata Karin Wani Labarin:Yadda aka yi jigilar Uranium a asirce daga Venezuela zuwa Amurka
Rundunar ta ce an ƙwato gudumar da ake zargin an yi amfani da ita wajen kai harin da kuma igiyar USB, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a kotu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chosu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da hukunta masu aikata laifi.
Ga hotunan kayan da aka ƙwato a hannunsa:
