Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sabon mafi karancin albashi na N71,000 ga ma’aikatan jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook a ranar Talata.
Yusf ya ce matakin ya yi daidai da kudurin gwamnatinsa na tabbatar da adalci da inganta rayuwar ma’aikatanmu.
“A bisa kudurinmu na tabbatar da adalci a zamantakewa da inganta rayuwar ma’aikatanmu, mun amince da Naira 71,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi a jihar Kano.”
Karanta Karin Wani Labarin: Kasafin 2025: Gwamnan Kano ya gabatar da N549bn ga Majalisa
Gwamnan ya ce, sabon mafi karancin albashi, wanda zai fara aiki daga watan Nuwamba, zai kara wa jihar albashin wata-wata da Naira biliyan 6 a matakin jiha da kuma naira biliyan 7 ga kananan hukumomi.
Ya bayyana cewa, “Bugu da kari, bayan karin girma ga malamai 20,737 da gwamnatinmu ta yi, an samu karin adadin da ya kai sama da naira miliyan 340 a albashinsu.
“Har ila yau, ina yaba wa kwamitin aiwatar da mafi karancin albashi na jihar kan aikin da ya dace da shi. – AKY,” ya buga.