An rufe jami’ar FUDMA bayan zanga-zangar dalibai
Hausa

An rufe jami’ar FUDMA bayan zanga-zangar dalibai

jami'ar

Hukumomi a Jami’ar Tarayya da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina ta rufe jami’ar biyo bayan zanga-zangar dalibai sanadiyyar halbe wani dalibin jami’ar.

Karanta karin Wani labarin: ‘Yan sanda sun tsare Jami’an da ake zargin sun azabtar da dalibin Jami’a har lahira

Rahotanni sun ce jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force da ke aiki a yankin sun halbi dalibai biyu, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar daya daga ciki.

Wani ganau ya shaidawa Jaridar PUNCH cewa daliban masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Dutsinma zuwa Katsina tare da kona tayoyi.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *