Jami’an ‘yan sanda na Dibishin Ganmo dake Kwara ne suka ja dalibin mai suna Suleiman Olayinka a kasa a lokacin da ya sauka daga kan babur ya karbi kudi a hannun abokinsa na POS, inda suka ci zarafinsa duk da cewa yana fama da ciwon asma.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, Eijire ya ce jami’an ‘yan sanda sun kama wanda abin ya shafa ne biyo bayan rahoton yaudara da kuma karya da aka yi masa.
Karanta Karin Wani Labarin: Kasar Equatorial Guinea ta haramta yin jima’i a ofisoshin gwamnati
“Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara na sane da wannan mummunan lamari wanda ya yi sanadin mutuwar Suleiman Olayinka mai shekaru 27.”
“An kai karar marigayin Nan take aka yi cikakken bayani ga jami’an ‘yan sanda don gudanar da bincike kan lamarin,” in ji Ejire.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne hukumomin ‘yan sanda a jihar suka kori jami’ai 3, Insifeto Abiodun Kayode, Insifekta James Emmanuel, da Sajan Oni Philip da aka gano a cikin kisan gilla da aka yi wa dalibin kwalejin fasaha ta jihar Kwara, Qoyum Abdulyekeen.