China yanzu ƙasa ce da lebura ke da karatun digiri na biyu a fannin ilimin Physics, Mai share-sharen gida ƙwararre a fannin muhalli, inda kuma mai karatun digiri na uku a fitacciyar Tsinghua ya ƙare a aikin ɗansanda.
Waɗannan hujjoji ne na gaske a yanayin tattalin arziƙin da ke fama da matsala – kuma babu wahala a samu irinsu da dama.
“Aikin da nake buri shi ne fanni saka a jari a banki,” in ji Sun Zhan a yayin da yake shirin soma aikin mai kawo abinci a wani gidan abinci da ke birnin Nanjing da ke kudanci.
Ɗan shekara 25 bai daɗe da kammala digirinsa na biyu ba a fannin nazarin kuɗi. Ya yi fatan samun kuɗi da yawa a wani babban aiki, amma ya ya ƙara da cewa, “na nemi irin wannan aikin, amma ba wani sakamakon kirki.”
Miliyoyin ɗalibai ne ake yayewa da suka kammala digiri a China duk shekara, a fannoni da dama, amma kuma babu guraben aiki.
Tattalin arzikin ƙasar na fuskantar ƙalubale da taɓarɓarewa a fannoni da dama, haɗi da fannin gidaje da samar da abubuwa.
Alƙalummar yawan matasa marar aikin yi ya kai kashi 20 kafin sauya alƙalumman domin nuna cewa komi na tafiya daidai.
A watan Agustan 2024 ya kai kashi 18.8. Sabbin alƙalumman watan Nuwamba sun dawo ƙasa da kashi 16.1.
Ɗaliban Jami’a da dama da suka kammala digiri, na shan wahala kafin su samu aikin yi a fannonin da suka karanta, kuma yanzu sun koma yin aikin da iliminsu ya fi ƙarfinsa, wani abu da ya zama abin faɗe ga ƴan’uwa da abokai.
Lokacin da Sun Zhan ya fara aiki a gidan abinci, iyayensa ba su daɗi ba.
“Ra’ayin iyayena wata babbar damuwa ce a gare ni. Bayan na shafe shekaru ina karatu kuma na tafi makaranta mai kyau,” in ji shi.
Ya ce iyayensa suna jin kunyar aikin da yake yi, sun fi son ya yi aikin gwamnati, amma ya ce “wannan ne zaɓi na.
Amma ya ce yana da wani tsari da musamman. Zai yi amfani da lokacinsa na gidan abinci ya koyi sana’ar gidan abinci domin ya buɗe nasa.
Ya ce idan har ya buɗe nasa kasuwancin, zai rufe bakin adawar da iyayensa ke yi da aikinsa.
“Aiki babban ƙalubale ne musamman a tsakiyar China, don haka nake ganin matasa da dama suke sauya tunani,” a cewar Farfesa Zhang Jun ta Jami’ar Hong Kong.
Ta ce ɗalibai da dama suna son samun digiri domin samun makoma mai kyau, amma kuma matsalar aiki babbar damuwa gare su.
“Samun aikin yi da wahala,” a cewar Wu Dan ƴan shekara 29 wadda yanzu mai bayar da horo ce a wata cibiyar yin wasannin tausa a Shanghai.
“Ga waɗanda muka yi karatun digiri na biyu da dama, karon farko kenan da suke farautar samun aiki, amma ƙalilan ne ke dacewa.”
Ta ce ba ta taɓa tunanin a haka za ta ƙare ba bayan kammala digiri a Jami’ar kimiya da fasaha ta Hong Kong.
Ta yi burin yin aiki a wani kamfanin kula da kaɗarori mai zaman kansa, ta samu aikin amma ba ta gamsu da sharuɗɗan ba.
Ta ƙi amincewa da aikin maimakon haka ta koma yin aiki a wata cibiyar kula da waɗanda suka ji rauni wajen wasanni, kuma danginta sun yi na’am da hakan.
“Sun yi tunanin zan samu aiki mai gwaɓi, kuma karatun da na yi ana ribibinsa. Sun kasa fahimtar dalilin da ya sa na karɓi wannan aikin da za a biya ni kuɗi kaɗan.”
Ta amince cewa akwai wahala rayuwa a Shanghai da albashin da take karɓa, sa’ar da ta ci ma saboda abokin zamanta shi yake da gidan da suke ciki.
Ta ce tana jin daɗin aikin na kula da waɗanda suka ji rauni a wajen wasanni, kuma tana fatan wata rana za ta buɗe irin cibiyar.
Ana tilasta wa masu digiri a China sauya tunaninsu musamman kan abin da suka ɗauka aiki mai kyau,” In ji Farfesa Zhang.
Wani abu ne da ake ganin “gargaɗi ne ga matasa, galibin kamfanoni a China haɗi da kamfanonin fasaha, kamar yadda ta bayyana.
Ta ƙara da cewa muhimman wurare na tattalin arziki waɗanda a baya ke diɓar masu digiri, yanzu sun koma bayar da aiki da wasu sharuɗɗa, kuma babu guraben ayyukan a wuraren a yanzu.
Yayin da kuma suke ƙoƙarin samar wa kansu makoma, yanzu masu digiri sun koma shiga hakarar fim da talabijin.
Manyan finafinai na buƙatar mutane da za su cike guraɓen fim, kuma a China musamman a Hengdian da ke kudu maso yammacin Shanghai akwai matasa da dama da ke neman aikin fitowa a fim.
“Nakan tsaya kusa da tauraron fim, an gane ni kusa da babban tauraro, ba tare da ba ni umarni ba,” in ji Wu Xinghai, wanda ya karanta fannin iginiyancin laturoni, kuma yanzu ya koma fitowa fim a matsayin maigadi.
Matashin ɗan shekara 26 ya yi kansa dariyar cewa saboda kyakkyawar fuskarsa ya samu shiga fim.
Ya ce mutane na zuwa Hengdian domin samun aiki na wasu watanni.
Ya ce wannan aikin wuccin gadi ne da ya dace da shi, kafin ya samu aiki. “Ba ni samu wasu isassun kuɗi amma kuma na samu kwanciyar hankali.”
“Wannan shi ne yanayin da China ke ciki, da zarar ka kammala digiri, ka zama marar aikin yi,” in ji Li, wanda ya ƙi bayyana cikakken sunansa.
Ya yi aikin bayar da umarni da rubuta labari kuma yanzu ya amince zai fito a wani fim na wasu watanni.
“Na zo nan ne domin neman aiki, duk da ina matashi. Idan na ƙara shekaru, zan samu tsayayyen aiki.”
Amma wasu da dama na fargabar ba zan samu aikin dole na tsaya saɓanin abin da suke tunani.
Rashin samun ƙwarin guiwa a tattalin arzikin China na nufin matasa ba su san makomarsu ba.
Wu Dan ko ƙawayenta da ke aiki ba su da tabbas.
“Suna cikin ruɗu tare da tunanin babu tabbas ga makomarsu. Waɗanda ke aiki ba su jin daɗinsa. Ba su san yaushe za su ci gaba da zama inda suke ba. Idan sun rasa aikin, wane aiki kuma za su yi?
BBC Hausa