Shugaban kasa Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministoci bakwai a ranar Litinin 4 ga Nuwamba, 2024 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a shafin sa na X a ranar Lahadi.
Karanta Wani Labarin: Rundunar Sojojin Najeriya ta kama wani dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Habu Dogo
Onanuga ya bayyana cewa shirin kaddamar da nadin ya biyo bayan amincewar da majalisar dattawa ta yi wa ministoci bakwai da aka nada a makon jiya.
Sabbin ministocin da mukamansu sun hada da Dr. Nentawe Yilwatda a matsayin ministar jin kai da rage talauci; Muhammadu Maigari Dingyadi a matsayin Ministan Kwadago & Aiki, da Bianca Odinaka Odumegwu-Ojukwu a matsayin Karamin Ministar Harkokin Waje.
Karanta Karin Wani Labarin: Kotu ta ba da belin ƙananan yara da gwamnatin Najeriya ta gurfanar kan zanga-zanga
Haka kuma a cikin gwamnatin Tinubu akwai Dakta Jumoke Oduwole a matsayin ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari; Idi Mukhtar Maiha a matsayin Ministan Dabbobi; Yusuf Abdullahi Ata a matsayin karamin minista a ma’aikatar gidaje da raya birane, sai kuma Dr. Suwaiba Said Ahmad a matsayin karamar ministar ilimi.