Rundunar sojin Najeriya ta gano wata masana’antar ƙera makamai a jihar Filato.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta ce ta gano masana’antar ne a cikin tsaunukan ƙauyen Pakachi da ke yankin ƙaramar hukumar Mangu.
Karanta Wannan ‘We’re Tired of Begging Nigerians Not to Revolt against Government’ – Sultan Of Sokoto
A lokacin samamen, sojojin sun ce sun samu makamai da wani kayayyakin ƙera makaman a masana’antar, tare da kama mutum guda da suke zargi da hannu a masana’antar.
Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar sojin na farautar wanda ake zargi da mallakar masana’antar domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Makaman da aka gano a masana’antar sun haɗar da:
Bindiga ƙirar AK 47 guda biyar.
Bindiga ƙirar gida 21
Ƙananan bindigogi 11 da harsasan su biyar.
Tukunyar sinadarin Carbide.
Saya guda uku.
Tarin nau’ikan harsasai daban-daban.
Guduma guda huɗu.
Mashina tono shida.
Injin janareto.
Da sauran abubuwa.