MTN ya nemi afuwar abokan hulɗarsa kan ɗaukewar sabis a Najeriya
Hausa

MTN ya nemi afuwar abokan hulɗarsa kan ɗaukewar sabis a Najeriya

MTN

Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya nemi afuwar aboka huldarsa sakamakon matsalar ɗaukewar sabis da kamfanin ya fuskanta a faɗin ƙasar.

Tun da tsakar ranar Laraba ne dai masu amfani da layin MTN suka fara fuskantar matsalar ɗaukewar sabis a layukansu.

Yadda masu kuɗi ke lalata ƴaƴan talakawa a Kano – Daurawa

Sai dai kamfanin cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce hakan ya faru ne sakamakon yankewar wasu wayoyin sadarwar kamfanin, lamarin ya ya shafi kira da kuma fannin intanet a layin.

Kamfanin ya kuma ce injiniyoyinsa na aiki domin shawo kan matsalar, inda ya ce sannu a hankali sabis ɗin ya fara dawowa a wasu yankuna.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *