Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa reshen asibitin kashi na Dala-Kano ta bukaci a sako abokiyar aikinsu Ganiyat Popoola da aka yi garkuwa da ita a watan Disamban bara a jihar Kaduna.
ClockwiseReports ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Dr. Aliyu Nura Muhammad ya yi wannan kiran ne a yayin wata zanga-zangar lumana da suka gudanar a harabar asibitin ranar Litinin.
Karin Wani Labarin: ‘Yan bindiga ke noma a gonakinmu a jihar Neja – Manoma
‘Yan kungiyar ta ARD karkashin jagorancin shugaban su, Dr. Aliyu Nura Muhammad sun zagaya asibitin a kafa suna rera wakokin dake bayyana rashin jin dadin su game da garkuwa da abokiyar aikinsu, Dr Popoola da dan uwanta da akai garkuwa dasu tare.
Dokta Muhammad wanda ya bayyana Dakta Ganiyat Popoola a matsayin likita mai kishin kasa kuma mai kwazo a cibiyar kula da ido ta kasa da ke Kaduna, ya ce ta sadaukar da rayuwarta wajen yi wa al’umma hidima duk da kalubalen da fannin kiwon lafiya ke fuskanta a Najeriya.
A cewarsa likitan da aka sace uwa ce mai ‘yaya biyar (5), sun bukaci da a sake ta ba tare da wani sharadi ba.
Karin Wani Labarin: Gwamnan Kano Bai San An Bayar Da Kwangilar Magani Ba Sai Bayan Fitar Bidiyon Dan Bello – Jaafar Jaafar
Ya kara da cewa an sace Dr Papoola ne a watan Disamba, 2023 tare da mijinta da dan uwanta. Duk da cewa an saki mijin nata saboda bashi da lafiya, amma har yanzu Dr. Papoola da dan uwan ta suna tsare a cikin wani yanayi na rashin mutuntaka.
Dr Muhammad ya ce “Muna kira ga duk masu ruwa da tsaki da su tabbatar da dawowar abokiyar aikinmu ba tare da wani sharadi ba.
“Kafin yanzu mun yi kokarin ganin an sake ta da suka hada da biyan kudin fansa, amma hakan mu bai cimma ruwa ba.