Ƙungiyar Likitoci, NMA, reshen jihar Kano ta baiwa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar wa’adin awanni 48 da ya kori Kwamishiniyar Jin-ƙai da Walwalar Al’umma, Amina Abdullahi bisa zargin cin zarafin wata likita to ta tafi yakin aiki.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr Abdulrahman Ali da sakataren sa, Dr. Ibrahim D. Muhammad su ka fitar ta ce lamarin ya faru ne a ɓangaren yara na asibitin kwararru na Murtala Muhammad lokacin da likitar take duba marasa lafiya.
Karanta Karin Wani Labarin: Rikici na neman ɓarkewa tsakanin Kwankwaso da Abba bayan da gwamnan ya dena ɗaga wayar mai gidan nasa
A cewar NMA, Kwamishiniyar ta je asibitin ne tare da tawogar ta, inda ta ci zarafin likitar saboda ta ce mata babu magungunan da Kwamishiniyar ta tambaya.
NMA ta kara da cewa a lokacin da lamarin ta faru, likitar ita kaɗai ce ke duba marasa lafiya sama da 100, “amma aka ci zarafin ta saboda wani abu da bata da iko a kai.”
“Hakan ya nuna yadda masu rike da mukamin siyasa ke ba zarar da ofishin su kuma ya nuna irin matsalar da ake da ita a fannin lafiya.
“Saboda haka mun bakwa gwamnan Kano awanni 48 da ya sallami Kwamishiniyar. In ba haka ba, to lamarin ba zai haifar da ɗa mai ido ba domin za mu janye aiyukan mu,”