Gwamnatin tarayya ta sa asibitin AKTH a cikin jerin asibitoci da zasu amfana da rage farashin wankin ƙoda
Hausa

Gwamnatin tarayya ta sa asibitin AKTH a cikin jerin asibitoci da zasu amfana da rage farashin wankin ƙoda

Jerin

Gwamnatin tarayya ta gyara jeren sunayen asibitocin gwamnatin tarayya da zasu amfana da rage farashin wankin ƙoda a Najeriya.

Gwamnati ta ce ta dau mataki ne domin ceton rayuka, da rage radadin jiki da na kudi, musamman a tsakanin ‘yan Najeriya masu rauni.
Farashin wankin kodar a karkashin tsarin tallafin yanzu ya zama N12,000 sabanin N50,000 da ake a da.

Zaku iya tunawa cewa a farkon jerin cibiyoyin da gwamnatin tarayya ta fitar a watan Maris wadanda zasu amfana da ragin sun hada da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Ebute-Metta Legas, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Jabi, Abuja, Asibitin Kwalejin Jami’ar (UCH) Ibadan, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Owerri, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) Maiduguri.

Karanta Karin Wani Labarin: Burina shine naga na hada kan yan Jaridun Afrika – Shugabar Kungiyar Yan Jaridun Afrika Masu Magana Da Yaren Hausa

Sauran sun hada da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Abeokuta, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LUTH) Legas, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Azare, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) Benin, da Jami’ar Koyarwa ta Calabar (UCTH) Calabar.

An kaddamar da tallafin ne a watan Janairu a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Hakazalika, a wani sakon da hadiman shugaban kasa Sunday Dare da Daniel Bwala suka fitar a ranar Litinin, jerin sunayen ba wani asibiti daga jihohin Arewa maso Yamma, duk da cewa jihar Jigawa ce ke da daya daga cikin jihohin da ke fama da cutar a Najeriya.

Amma bayan rahoton da SolaceBase ta fitar na rashin sanya asibitocin jihohin da aka lissafa a sama, gwamnatin ta tarayya tasa wani babban asibitin tarayya a arewa maso yamma, Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) a cikin wadanda zasu amfana ta ragen.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ta hannun Alaba Balogun, Mataimakin Darakta / Shugaban, Watsa Labarai & Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ya tabbatar da saka AKTH din.

 

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *