Gwamnatin Kano ta janye dokar hana fita gaba ɗaya
Hausa

Gwamnatin Kano ta janye dokar hana fita gaba ɗaya

Abba Kabir Yusuf. Kano State, court Government has relaxed curfew imposed on the state from 6 AM to 6 PM.

Gwamnatin Jihar Kano, ta janye dokar hana fita da ta sanya, biyo bayan zanga-zangar matsin rayuwa da ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Baba Halilu Ɗantiye, ya fitar da yammacin ranar Litinin.
Idan ba a manta ba, ClockwiseReports  ta ruwaito yadda gwamnatin jihar, ta sanya dokar hana fita a jihar bayan da zanga-zangar da aka fara a ranar 1 ga watan Agusta, a faɗin ƙasar kan tsadar rayuwa ta koma tarzoma.

Karin Wani Labarin: ’Yan bindiga sun kashe matafiya 7 a hanyar Taraba
Daga baya Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya sassauta dokar daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 2 na rana.
Har wa yau, gwamnatin ta sake sassauta dokar daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

Ɗantiye, ya ce gwamnatin ta janye dokar ne gaba ɗaya, duba da yadda al’amura suka daidaita a jihar.
Kazalika, Kwamishinan ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.
Sannan ya roƙi su yi Kano addu’a domin samun dawamammen zaman lafiya da kuma ƙasa baki ɗaya.
Idan ba a manta ba, zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta fara ne a ranar 1 ga watan Agusta a faɗin Najeriya.

Sai dai zanga-zangar a jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, da wasu sassan Najeriya sun rikiɗe zuwa tarzoma.

Lamarin ya janyo asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa.

Daga bisani Shugaba Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi game da halin da suke ciki, amma jawabin bai gamsar da masu zanga-zangar ba.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *