A karon farko tun bayan fitar bidiyon da Dan Bello ya fitar kan wata badakalar kwangilar magani a Jihar Kano, Jaafar Jaafar, ya bayyana matsayarsa game da lamarin.
Jaafar Jaafar ya sha suka kan gum da bakinsa da ya yi bayan fitar bidiyon inda ya zargi wasu jami’an Gwamnatin Kano da karbar kudi a hannun kananan hukumomi domin yin kwangilar magani wanda yake ba bisa ka’ida ba.
Karin Wani labarin: PDP ta lashe dukka kujerun ciyamomi a zaɓen ƙanan hukumomi na jihar Bauchi
Jaafar Jaafar ya ce a binciken da ya yi kan harƙallar Novomed, tabbas gwamna bai san “Ministry of Local Government” ta ba da kwangilar ba har sai da Dan Bello ya fitar da bidiyon.
“Kwamishinan ma’aikatar, wanda shi ne mataimakin gwamna, shi ne wuƙa shi ne nama a harkar. Watakil saboda hukuncin “Supreme Court” da ta ba wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su, sai ciyamomi da “deputy governor” su ka yi amfani da damar su ka yi gaban kansu.” A cewarsa.
Har wa yau ya kara da cewa:
Karin Wani Labarin: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 16, ta lalata gidaje 3,936 a Jigawa
“Duk wanda ya san yadda gwamnati ke wakana, zai gane cewa akwai zummar yin babakere da kuɗin al’umma duk lokacin da ka ga ƙananan hukumomi sun fitar da kuɗi bai-ɗaya kuma a lokaci ɗaya.”
Sai dai a karshe ya bayyana cewa duk da cewa tabbas Gwamnan bai sani ba, amma dole jama’a du ɗora wa Gwamna laifi, domin shi su ka zaba a matsayin shugaba.