Ba shakka dawowar Trump a shugabancin Amurka abu ne mafi ɗaukar hankali a tarihin ƙasar, kasancewar bayan shekara huɗu da barinsa White House miliyoyin Amurkawa sun sake zaɓensa domin ya koma karo na biyu.
Abubuwan da suka faru a yaƙin neman zaɓen abubuwa ne da za su tabbatu a litattafan tarihi – ya tsira daga yunƙurin kashe shi sai biyu kuma ainahin abokin karawarsa a zaɓen Joe Biden ya fice daga takara ‘yan watanni kafin ranar zaɓe.
Karanta Karin Wani Labarin: Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ke shirin kai hari ga masu gyaran layin lantarkin Arewa
Duka da cewa ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u, amma yawancin Amurkawa a jihohin da ba su da tabbas sun zaɓe shi, inda jama’a da dama ke nuna damuwarsu kan batun tattalin arziƙi da kuma baƙi ‘yan cirani.
Nasararsa ta zo ne bayan matsaloli da ya faɗa – ya ki yarda da sakamakon zaɓen 2020, wanda ya faɗi a hannun Biden, da kuma har yanzu ana bincikensa kan rawar da ya taka a ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓen.
Yana fuskantar tuhuma kan angiza magoya bayansa su kai hari kan ginin majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun 2021. Kuma shi ne a tarihi shugaban Amurka na farko da kotu ta samu da laifin ƙarya a takardun harkokin kasuwanci.
Abu ne mai sauki a fahimci dalilin da ya sa yake mutum mai janyo raba kai.
A duk tsawon lokacin yaƙin neman zaɓensa ya riƙa furta kalamai na tsokana da tunzuri – inda yake barazanar ramuwar gayya a kan abokan hamayyarsa na siyasa da ire-irensu.
Karanta Karin Wani Labarin: Wutar Lantarki ta dawo a Arewa
Saƙonsa a kan tattalin arziƙi ya yi tasiri
Mutane da dama na ɗari-ɗari da shi – yawancin mutanen da na tattauna da su a lokacin yaƙin neman zaɓensa sun ce za su so su ga ya daina magana barkatai – amma duk da haka sun kawar da kai a kan wannan, inda suka mayar da hankali kan tambayar da yake yawan yi a wajen yaƙin neman zaɓensa – “Da rayuwarku ta shekara biyu baya da ta yanzu wacce ce ta fi?”
Saboda haka mutane da dama da na tattauna da su waɗanda suka zaɓi Trump sun yi ta nanata min cewa suna ganin tattalin arziƙin Amurka ya fi kyau lokacin da Trump ke kan mulki, kuma yanzu rayuwa ta yi musu tsada.
Duk da cewa yawancin matsalolin saboda wasu abubuwa ne na waje kamar annobar Korona, amma mutanen na ɗora ailhaki a kan gwamnati mai barin gado.
Haka kuma masu zaɓen sun damu sosai da maganar baƙin haure, inda aka samu yawan da ba a taɓa samu ba a lokacin Biden.
‘Amurka farko’ a mulki na biyu na Trump
“Amurka farko” wanda ya kasance ɗaya daga cikin taken da Trump ya yi amfani da su a yakin neman zaɓensa ya ja hankalin masu zaɓe sosai.
A duk fadin ƙasar kama daga ɓangaren masu ra’ayin riƙau, da masu ra’ayin kawo sauyi, na jin yadda jama’a ke ta ƙorafi kan biliyoyin dala da ake kashewa wajen taimakon Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha – maimakon haka suna ganin kamata ya yi a kashe kuɗin a cikin gida.
Karanta Karin Wani Labarin: ‘Yan sanda sun kama ‘yan kasashen waje 113, ‘yan Najeriya 17 bisa zargin aikata manyan laifuka ta yanar gizo
Saboda haka jama’a na ganin idan suka zaɓi Harris, wadda take mataimakiyar shugaban ƙasa a gwamnatin Biden, abin zai ci gaba ne – suna buƙatar sauyi.
Lokacin da ya hau mulki a karon farko a 2016, baƙo ne a fagen zuwa wani ɗan lokaci, inda ya zagaye kansa da tsofaffi kuma fitattun masu bayar da shawara da tsara dabaru waɗanda suke taka masa burki a kan wasu abubuwa. Amma a yanzu kusan ya nuna ba shi da sha’awar bin dokoki da tsare-tsaren yadda ya kamata.
Da dama daga cikin waɗannan masu bayar da shawara sun soke shi- wasu sun kira shi maƙaryaci, ɗan kama-karya, wasu sun ce bai dace da shugabancin ba – sun yi gargaɗin cewa idan har ya sake kewaye kansa da masu goyon bayansa ‘yan-ga-ni-kashe-ni – abin da kuma ake tsammanin zai yi , to kenan ba wanda zai tsawatar masa, ko ya taka masa birki a kan tsauraran manufofinsa.
A lokacin da bar mulki ya fuskanci tarin shari’o’i na miyagun laifuka a kan rawar da ya taka kan kutse a majalisar dokokin Amurka, da yadda ya tafiyar da batun takardun tsaro na ƙasa na sirri da kuma maganar kuɗin toshiyar-baki da aka ba wata fitacciyar mai fim ɗin batsa, aka ce ya bayar domin hana ta fallasa shi
Sai dai tun da kotun ƙolin Amurka ta zartar da cewa shugaban ƙasa yana da rigar kariya daga gurfana a gaban kotu kan abubuwan da ya yi lokacin yana kan kujera, zai zama gagarumin aiki ga duk wani mai gabatar da ƙara ya tuhume shi a lokacin mulkinsa mai zuwa.
Haka kuma a matsayinsa na shugaban ƙasa zai iya umartar ma’aikatar shari’a ta yi watsi da tuhumar da ake yi masa ta tarayya kan tarzomar da aka yi a majalisar dokoki a ranar 6 ga wata, yadda ba zai damu ba kan yanke masa hukuncin ɗauri.
Haka kuma zai iya a matsayinsa na shugaban ƙasa yafe wa ɗaruruwan mutanen da aka ɗaure kan kutsen majalisar dokokin.
A ƙarshe dai masu zaɓe sun kasance da zaɓi biyu na Amurka.
Donald Trump ya gaya musu cewa Amurka ta kama hanyar rugujewa kuma shi kaɗai ne zai sake bunƙasa ta.
Ita kuwa Harris ta yi gargaɗi ne da cewa idan aka sake zaɓar Trump hatta dumukuraɗiyyar Amurka za ta fuskanci haɗarin gushewa.
Karanta Karin Wani Labarin: MTN ya nemi afuwar abokan hulɗarsa kan ɗaukewar sabis a Najeriya
Yanzu dai za a zuba ido a gani. Amma abin da shi kansa Trump ya faɗa a lokacin yaƙin neman zaɓensa bai kawar da fargabar da jama’a ke yi ba.
Ya riƙa yabo da kambama shugabannin da ake gani masu kama-karya ne irin su Vladimir Putin na Rasha da kuma Kim Jong Un na Koriya ta Kudu.
Sannan ya yi magana a kan ƙoƙarin rufe bakin masu sukarsa a kafafen yaɗa labarai.
Kwanaki kaɗan kafin zaɓen ya yi wasu kalamai da ke nuna cewa ba zai damu ba idan aka kashe ‘yanjarida.
Kuma ya ci gaba da maganganu da zargin maguɗi marassa tushe – duk da cewa a ƙarshe zaɓen ya kai shi ga nasara.
Yanzu dai masu zaɓe za su tantanace maganganun da ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe – waɗanne ne na gaskiya waɗanne ne kuma romon-baka – kamar yadda aka san shi da yi.
Kuma a sani cewa fa lalle, ba Amurkawa kaɗai ba ne za su fuskanci gaskiyar lamari kan mulkin na Trump na wa’adi na biyu ba.
Karanta Wani Labarin: Rikici na neman ɓarkewa tsakanin Kwankwaso da Abba bayan da gwamnan ya dena ɗaga wayar mai gidan nasa
A yanzu sauran sassan duniya za su fahimci aihanin abin da takensa na “Amurka Farko” ke nufi.
Kama daga matsalolin tattalin arziƙi da suka biyo bayan ƙarin kashi 20 cikin ɗari na haraji da ya tsara sanya wa a kan kayan da za a shiga da su Amurka, har zuwa ga yaƙe-yaƙen da ake yi a Ukraine da Gabas ta Tsakiya da ya lashi takobin kawowa ƙarshe – ko da kuwa wane ɓangare ne ya yi nasara.
Donald Trump bai iya samun dama ya aiwatar da dukkanin manufofi da shirye-shiryensa ba a wa’adinsa na farko.
Yanzu tun da ya samu wa’adi na biyu da kuma rashin nauyi da yawa a kansa, Amurka da duniya za su ga ainahin abin da zai iya yi.
(BBC Hausa)