Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga matasan Najeriya da ɗalibai su guji amfani da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi, yana mai cewa irin waɗannan kwayoyi ba sa ƙara wa rayuwa wata daraja sai dai lalata ta kawai.
Ya yi wannan jawabi ne a Abeokuta, Jihar Ogun, yayin taron gangamin yaki da miyagun kwayoyi na biyu da ake kira ‘Fly Above The High’ wanda Kungiyar Recovery Advocacy Network ta shirya.
Obasanjo ya kuma tuna cewa ƙoƙarin fara shan sigari a lokacin da yake saurayi ya jawo masa matsananciyar tari, wanda ya sa ya gudu daga wannan ɗabi’a.
“Idan da na nace, da na zama mai ta’ammali. Da zarar ka shiga, da wuya ka fita,” in ji Obasanjo ga taron da ya haɗa matasa, ɗalibai, ƙwararrun masu kula da lafiyar hankali, da masu tsara manufofi.
Tsohon shugaban kasar ya jaddada cewa, “Babu wani abu da miyagun kwayoyi za su yi maka sai lalata rayuwarka.”
Ya kuma shawarci waɗanda suka riga sun zama masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da su nemi taimako, tare da yin gargaɗi ga al’umma su guji tsangwama ko wulaƙantar da su.