Wani ayarin sojojin Venezuelan ya yi tafiyar kilomita 160 (mil 99) daga Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Venezuelan (IVIC), wadda ke wajen birnin Caracas, zuwa tashar jiragen ruwa ta Puerto Cabello a cikin jihar Carabobo.
Dalilan da ke tattare da tafiyar da daddare da kuma tsananin sirrin ya bayyana ne kwanaki kaɗan bayan haka: Sojoji na rakiyar wata motar da ke ɗauke da kwantena mai kusan kilogiram 13 na sinadarin Uranium da aka inganta sosai, wanda za a kai ƙasar Amurka.
Aikin ya shafi gwamnatocin Amurka da Venezuela da Birtaniya, da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, wadda a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 8 ga watan Mayu, ta bayyana shi a matsayin “aikin haɗin gwiwa da aka tsara a tsanake, wanda aka gudanar ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro”. An lura cewa irin wannan nau’in kayayyakin nukiliya na iya haifar da haɗarin yaɗuwa ko barazanar tsaro idan ya faɗa hannun da bai dace ba.
Karanta Karin Wani Labarin: Anfanin Dankalin Hausa a jikin Dan Adam
13kg wani kaso ne ɗan ƙalilan idan aka kwatanta da fiye da kilogiram 400 da aka yi iƙirarin Iran ta mallaka kafin fara yaƙinta da Amurka da Isra’ila. Sai dai alaƙar gwamnatin Venezuela da Iran da Rasha da Cuba da kuma Koriya ta Arewa ta kasance abin damuwa ga gwamnatin Amurka kuma a cewar ƙwararrun da suka zanta da BBC Verify, har da ma da hukumar IAEA.
Jack Crawford, na Royal United Services Institute (Rusi), ya shaida wa BBC Verify cewa wannan cire yranium ɗin da aka yi wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙasashen duniya na tabbatar da ingantaccen sinadarin uranium – wanda aka sarrafa da nufin amfani da shi don samar da ababen more rayuwa na faraen hula – ba za a iya faɗaqwa hannun kasashe ko kuma wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke neman kera makaman kare dangi ba.
Ya ce duk da cewa uranium da aka cire ya ƙunshi fiye da kashi 20% na uranium-235 – kuma ana ɗaukar HEU da ya kai matakin a 90% zuwa sama a matsayin wanda ya kai matakin haɗa makami – “ya isa a ƙara tace shi don samar da ƙaramin makamin nukiliya”.
Don haka ta yaya Venezuela ta sami ingantacciyar uranium, kuma me ya sa ta miƙa shi ga Amurka.
