Gwamnatin Kano ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu
Hausa

Gwamnatin Kano ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430 1.jpeg

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Juma’a, 12 ga Satumba, a matsayin ranar hutu domin bikin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Hutun dai ya zo daidai da bikin Maulud, wanda ya yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1447 bayan Hijira.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa Labarai da harkokin cikin Gida na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Alhamis a Kano.

Waiya ya yi kira ga ma’aikata, ‘yan kasuwa da al’umma baki ɗaya da su yi amfani da hutun cikin zaman lafiya tare da bin koyarwar Annabi (SAW).

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai, hakuri da biyayya, tare da yin addu’a domin samun zaman lafiya da cigaba.

Gwamnati ta mika sakon taya murna, tana yi wa jama’a fatan bikin Maulud mai cike da zaman lafiya.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *