Fitar da maniyi akai-akai na rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mafitsara – Masana
News

Fitar da maniyi akai-akai na rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mafitsara – Masana

1757264809269

Koodinetan Shirin Yaƙi da Cutar Sankara na Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a, Dakta Uche Nwokwu, ya bayyana cewa yawan fitar maniyyi na iya rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mafitsara ga maza.

Nwokwu ya bayyana haka ne a yau Lahadi a Abuja, yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, domin mayar da martani kan batun da ya karade a kafafen sada zumunta cewa maza suna buƙatar fitar da maniyyi sau 21 a wata domin guje wa cutar prostate.

Ya yi bayani cewa gudanar da wasu al’amurra na rayuwa, ciki har da yawan fitar maniyyi, na iya taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da cutar jejin mafitsara.

Yana nuni da wani babban bincike da aka gudanar a 2016, wanda aka wallafa a mujallar Journal of the American Medical Association (JAMA), inda ya bayyana cewa maza da suka bada rahoton sun fitar da maniyyi sau 21 ko fiye a wata tun suna shekaru 20 zuwa 40, sun fi ƙarancin kamuwa da cutar.

Ya ce binciken ya gano cewa irin waɗannan maza sun rage haɗarin kamuwa da cutar da kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da waɗanda ke fitar da maniyyi sau huɗu zuwa bakwai kacal a wata.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *