Yan sandan Kano sun kama mutum 17 da zargin shirya zanga-zanga
Hausa

Yan sandan Kano sun kama mutum 17 da zargin shirya zanga-zanga

sun

Rundunar ‘yansandan Najeriya a jihar Kano ta ce ta kama mutum 17 kan zarginsu da aikata daba da kuma shirya zanga-zanga.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce bayanan sirri da ta tattara ne suka ba ta nasarar kama mutanen, amma ba ta bayyana dalilin shirya zanga-zangar ba.

Sai dai bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa wasu matasa sun taru a kusa da gidan sarki na Nassarawa, wanda Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ke ciki, kafin ‘yansanda su tsarwatsa su da safiyar yau Laraba.

Karanta Karin Wani Labarin: Kasafin 2025: Gwamnan Kano ya gabatar da N549bn ga Majalisa

“Bayan samun bayanan sirri game da shirin zanga-zangar tayar da fitina da wasu ke yi, ‘yansanda tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun fita wasu muhimman wurare a ƙwaryar birnin Kano domin daƙile zanga-zangar,” a cewar sanarwar.

Har yanzu batun masarautar Kano na ci gaba da jan hankalin mazauna jihar, inda Aminu Ado da Muhammadu Sanusi ke bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *