Yanzu haka ƙudirin sabuwar Dokar Haraji ya tsallake karatun farko a Majalisar Dattawan Najeriya.
Majalisar Dattawa ta amince a yi wa ƙudirin sabuwar dokar harajin karatu na biyu bayan zazzafar muhawara da aka tafka a yayin karatun farko.
ClockwiseReports ta ruwaito cewa, an yi wa ƙudirin karatun farko bayan Sanata Opeyemi Bamidele na jam’iyyar APC mai wakiltar Ekiti ta Tsakiya ya gabatar da shi a ranar Alhamis.
Ƙudurin Dokar Haraji na ci gaba da tayar da ƙura a Najeriya inda yake ta faman shan suka daga ɓangarori da dama, musamman daga Gwamnonin da Sarakunan Arewa.
A bayan nan ne dai Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Tarayya ƙudirin sabuwar Dokar Harajin wanda yake neman a gaggauta zartar da ita domin ta soma aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.
Gwamnatin Tinubu dai na ci gaba da nanata cewa tana son tabbatar sabon tsarin harajin daga cikin matakan da take ɗauka na saita tattalin arzikin kasar duk da shawarar Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya na dakatar da kuɗirin.
Gwamnati ta ce babban dalilin sabuwar dokar shi ne sake fasalin yadda ake karɓar harajin domin kawo ƙarshen ƙalubalen da gwamnati ke fuskanta kamar harajin birane daban-daban, rage nauyin harajin daga kan ɗaiɗaikun ’yan ƙasa da kasuwanci tare da taimakawa wajen kasuwanci domin samar da tattalin arziki da makoma mai kyau ga Najeriya.