‘Yan sandan Kano sun kama ƴan daba 22 da suka addabi Ɗorayi
Hausa

‘Yan sandan Kano sun kama ƴan daba 22 da suka addabi Ɗorayi

kano police

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar da kama mutum 22 da ake zargi riƙaƙƙun ƴan daba ne a unguwar Ɗorayi da ke jihar.

Matakin ya zo ne sakamakon ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan daba a unguwar ranar Laraba.Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya nuna yadda aka ji wa wasu matasa raunuka a arangamar da aka yi.

Karin wani Labarin Yadda masu kuɗi ke lalata ƴaƴan talakawa a Kano – Daurawa

Cikin wani bidiyo da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ƴan sanda sun bayyana sunan wasu mutum 30 da ake zargi ƴan daba ne da suka addabi Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale.

A cewar kakakin rundunar, kwamishinan ƴan sanda na jihar Muhammad Usaini Gumel zai buɗe sabon ofishin yaƙi da ayyukan daba a unguwar ta Ɗorayi.

Rundunar ta ƙaddamar da shirin tuba da gyara halin wasu ‘yan daba a Kano, har ma ta ɗauki wasu kusan 50 aiki bayan sun tuba.

Kazalika, rundunar ta sha shirya wasanni tsakanin tubabbun ‘yan dabar da kuma ma’aikatanta a matsayin wani sabon salon yaƙi da halayayyar ta daba.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *