‘Yan majalisar NNPP sun amince da tsige Ali Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye
Hausa

‘Yan majalisar NNPP sun amince da tsige Ali Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye

Rep. Ali Madaki and Rep. Tijjani Jobe 696x529

‘Yan majalisar wakilai 15 cikin 18 da aka zaba a jam’iyyar NNPP, sun amince da tsige dan majalisa mai wakiltar Dala, Ali Madaki, a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.

A cikin wata takarda da jaridar DAILY NIGERIAN ta gani a ranar Litinin, ‘yan majalisar da ba su saka hannu ba su ne mambobin Dala, Rano/Kibiya/Bunkure da Karaye/Rogo — Ali Madaki, Alhassan Rurum da Abdullahi Sani.

A cikin wata wasika da aka aika zuwa ga kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, tare da hadin gwiwar shugaban jam’iyyar NNPP da sakataren jam’iyyar NNPP Ajuji Ahmed da Dipo Olayoku, shugabannin jam’iyyar sun gabatar da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado. Tijjani Jobe, a matsayin wanda zai maye gurbin Mista Madaki.
“Jam’iyyar NNPP na fatan mika gaisuwa gare ku, shugabanni da daukacin ‘yan majalisar wakilai.

“Jam’iyyar ta lura da kyakkyawar alakar da ta wanzu a tsakaninmu, kuma mun kuduri aniyar dorewar hakan.

“Mun rubuta wannan wasika ne domin mika sunan babban dan jam’iyyar, HON TUJANI ABDULKADIR JOBE domin maye gurbin Hon Aliyu Sani Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.

“Muna addu’ar ku da ku yi gaggawar daukar wannan wasikar bisa la’akari da muhimmancinta ga jam’iyyarmu, da ‘yan kwamitinta a majalisa, da kuma mai girma majalisar wakilai baki daya.

Duk da cewa ba a bayar da dalilin tsige Mista Madaki ba, jaridar clockwisereports ta ruwaito cewa kwanan nan Mista Madaki ya yi tir da yunkurin Kwankwasiyya, kuma ya yi mubaya’a ga uban jam’iyyar, Boniface Aniebonam.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *