Yan bindiga sun yi wa manoma 10 kisan-gilla a jihar Neja
Hausa

Yan bindiga sun yi wa manoma 10 kisan-gilla a jihar Neja

Bandits, Corps, community, Taraba, Yan, Jalingo

Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Wayam da Belu-Belu a Ƙaramar Hukumar Rafi da ke Jihar Neja, inda suka kashe aƙalla manoma 10, ciki har da mata, sannan suka sace wasu.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa an sare kan mutum shida daga cikin waɗanda aka kashe.
Hakazalika sun ce maharan sun jikkata wasu da dama.
Bala Tukur, ɗaya daga cikin mazauna yankin, ya bayyana cewa, “Sun kashe mutum 10 ba tausayi. Kowa ya tsere. Samun damar girbe amfaninmu yanzu zai yi wuya.”

Karanta Karin Wani Labarin: An Dage Gasar Cin Kofin Makarantun Sakandare na Gombe

Harin ya kawo cikas ga aikin noma a yankunan, inda wasu mazauna yankin aka tilasta musu biyan kuɗin haraji kafin shiga gonakinsu don girbe amfanin gona.

’Yan bindigar sun kuma kai hari garin Zungeru inda suka sace mutane da dama, ciki har da Indiyawa biyu da ke aiki a gonar shinkafa a Borgu.

Gwamnatin Jihar Neja, ta sanar da cewa tana sane da lamarin, inda Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed ya yi ƙarin haske kan lamarin.

Ya ce, “An tura jami’an tsaro domin su magance matsalar da kuma hana ta sake faruwar hakan a gaba.”

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *