Yan bindiga sun harbe wasu matafiya guda bakwai har lahira a safiyar Litinin a kan babbar hanyar Takum zuwa Wukari da ke Jihar Taraba.
Kisan gilla da aka yi wa matafiyan da direban motarsu ya haifar da zaman dar-dar a yankin Takum.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ɗauƙacin matafiyan waɗanda ’yan garin ne, suna hanyarsu ta zuwa garin Sa’ayi da ke Jihar Binuwai ne lokacin da harin ya rutsa da su a tsakanin garin Chanchangin da garin Wukari.
Wani shaida ya ce maharan sun buɗe wa motar wuta ne suka kashe duk mutanen da ke cikinta, nan take, amma ba su ɗauki komai ba a cikinta.
Karin Wani Labarin: Harda Aljanu a Zanga-zangar Kano – Dakta Kachako
Ya yi zargin maharan na daga cikin ’yan ta’addan da suka addabi dazukan da ke tsakanin Jihar Binuwai da Jihar Taraba.
A kan wannan hanya ce dai aka kashe basaraken garin Chanchangi da babban ɗansa a watan Yuli.
Hanyar ta zamo tarkon mutuwa saboda ayyukan ’yan ta’adda da ke yin fashi da kuma garkuwa da matafiya domin karɓar kuɗin fansa a cikin dare da rana.
Wakilinmu ya tuntuɓi kakakin ’yan sandan jihar Taraba, DSP kwach, game da harin na safiyar Litinin, amma jami’in ya ce masa sa zai bincika.