Rahotanni sun bayyana cewa wutar lantarki da a bayan nan ta yi nisan kiwo ta dawo a wasu jihohin Arewacin Nijeriya.
ClockwiseReports ta ruwaito cewa, an samu wutar lantarkin da yammacin wannan Larabar a jihohin Filato da Bauchi da Gombe da kuma Benuwe.
Karanta Karin Wani Labarin: Kasafin 2025: Gwamnan Kano ya gabatar da N549bn ga Majalisa
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mazauna birnin Jos da ke Jihar Filato sun shiga sowa da farin cikin bayan dawo da wutar lantarkin da misalin ƙarfe 7:20 na yammacin wannan Larabar.
Bayanai sun ce an shafe aƙalla kwanaki 10 babu wutar lantarki a jihohin Arewa da dama, lamarin da ya tsayar da harkokin kasuwanci bayan katsewar tashar samar da wutar lantarki da ke jihohin Benuwe da Enugu.