Tsohon Shugaban INEC Ya Bukaci A Dai na Bawa Ma’aikatan Gwamnati Mukaman Gargajiya
Hausa

Tsohon Shugaban INEC Ya Bukaci A Dai na Bawa Ma’aikatan Gwamnati Mukaman Gargajiya

jega 1

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Attahiru Jega ya ce ya kamata a hana ma’aikatan gwamnati karbar mukaman gargajiya a lokacin da suke aikin gwamnati domin dakile yawaitar ayyukan cin hanci da rashawa.

Jega ya yi wannan kiran ne a ranar Larabar da ta gabata a taron tattaunawa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC tare da manyan jami’an hukumomin gwamnati, kan hana cin hanci da rashawa a cikin ma’aikatan gwamnati a Abuja.

A cewarsa, wani abin takaici ne ga mahukuntan gargajiya na ba da mukamai ga jami’an gwamnati.

Tsohon shugaban hukumar ta INEC ya ce, “daukar mukami na gargajiya a bawa jami’in gwamnati ya sa shi ya zama mai saurin cin hanci da rashawa da kuma zagon kasa ga aikin sa.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *