Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a fadin ƙasar.
Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda.
An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar.
Sai dai kuma an cire manyan asibitocin gwamnatin tarayya da ke jihohin Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar.
SolaceBase ta tattaro cewa jihar Jigawa tana daya daga cikin mafi girman jihar da ake dama da cutar koda a Najeriya.