SSANU, NASU sun janye yajin aiki na tsawon wata daya
Hausa

SSANU, NASU sun janye yajin aiki na tsawon wata daya

1 SSANU NASU

Kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin ma’aikatan da ba na koyarwa a manyan makarantu, ya ce ya dakatar da yajin aikin da suke yi na tsawon wata daya, daga ranar 5 ga watan Nuwamba. SSANU

JAC ta ƙunshi Ƙungiyar NASU da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU).

Karanta Karin Wani Labarin: Ina samun N2.4m duk shekara a harkar bara – Habib Ibrahim

Mista Peters Adeyemi, babban sakataren kungiyar ta NASU ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Mista Mohammed Ibrahim, shugaban kungiyar SSANU ya sanya wa hannu ranar Lahadi a Abuja.

Idan za a iya tunawa JAC ta umurci mambobinta da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 28 ga Oktoba, domin neman rashin biyan albashin watanni hudu da kuma rashin aiwatar da wasu bukatu.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *