Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tafi Saudiyya, domin halartar Taron Haɗin Kan Ƙasashen Larabawa da Musulunci.
Hadimin Shugaban Ƙasa Kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa.
Ya ce, “Shugaba Tinubu zai yi magana kan rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda zai jadadda buƙatar a tsagaita wuta da kuma nemo mafita.
Karanta Wani Labarin: Uwargidan shugaban kasa Tinubu ta Karyata batun cewa ta shirya taron yiwa kasa addu’o’i
“Najeriya za ta kuma goyi bayan ci gaba da ƙoƙarin dawo da tsarin ƙasashen biyu a matsayin hanya mai ɗorewa ta samun zaman lafiya a yankin.”
Onanuga ya ƙara da cewa wasu manyan jami’ai za su raka Shugaba Tinubu, ciki har da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, da Darakta Janar na Hukumar Sirri ta Ƙasa (NIA), Mohammed Mohammed.
Bayan kammala taron, Shugaba Tinubu zai dawo Abuja.