Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, domin halartar taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci da za a yi, wanda zai tattauna batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya, musamman rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Karanta Karin Wani Labarin: Uwargidan shugaban kasa Tinubu ta Karyata batun cewa ta shirya taron yiwa kasa addu’o’i
Mataimakin Gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman ne ya tarbi Shugaba Tinubu a lokacin da ya isa.
Taron wanda aka shirya zai fara a ranar Litinin 11 ga Nuwamba, 2024, ana gudanar da shi ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.