Jami’an lafiya sun ce aƙalla Falasɗinawa goma ne suka mutu a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama kan wata makaranta da ‘yangudun hijira ke zaune a birnin Gaza.
Masu aikin ceto na ci gaba da aikin neman waɗanda ke da sauran numfashi da ke ƙarƙashin ɓuraguzai a makarantar ta Abu Assi a sansanin ‘yangudun hijira na Shati.
Ana ganin akwai mutane da dama da ɓuraguzai suka binne.
Har yanzu Isra’ila ba ta ce komai ba a kan harin..
Akwai kuma wasu mutane tara daban da suka rasu a wasu hare-haren na Isra’ila a birnin na Gaza.
Haka kuma a can Lebanon ma, ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta ce hare-haren Isra’ila a wani ƙauye da ke gabashin yankin Baalbek, sun kashe mutum shida da suka haɗa da yara uku.