Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar Bauchi, ta lashe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar 20 da aka gudanar ranar Asabar 17 ga watan Agusta.
Shugaban hukumar zaɓen jihar, Ahmed Makama, ne ya bayyana sakamakon a daren da ya gabata a birnin Bauchi.
Karin Wani Labarin: Gwamnan Kano Bai San An Bayar Da Kwangilar Magani Ba Sai Bayan Fitar Bidiyon Dan Bello – Jaafar Jaafar
To sai dai majiyar BBC da ke jihar ta tabbatar da cewa jam’iyyar APC mai hamayya a jihar ta yi watsi da sakamakon zaɓen tana mai bayyana shi a matsayin ”fashi kan ‘yancin masu zaɓe da cutar da tsarin dimokraɗiyya”.
Yayin wani taron manema labarai da jam’iyyar ta kira sakatariyarta da ke jihar, APCn ta zargi jam’iyyar PDP da jirkita sakamakon zaɓen.
Karanta Karin Wani Labarin: Mataimakin Gwamna Yusuf yayi murabus, ya koma APC
A watan da ya gabata ma dai, jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar Adamawa ta lashe duka zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomin jihar 21.
Masu rajin kare dimokraɗiyya a Najeriya kan soki yadda tsarin zaɓukan ƙananan hukumomi ke gudana a ƙasar, inda galibi jam’iyyar da ke mulkin jiha kan lashe zaɓe a duka ƙananan hukumomin da ke jihar.
Wani abu da suka ce yana barazana ga ‘yan cin gashin ƙananan hukumomin da Kotun Ƙolin ƙasar ta tabbatar a watan da ya gabata.