Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya fara wani yunkuri na karin farashin kudin kira da na sayen data ga kwastomominsa dake Nijeriya.
Karin Wani Labarin: MTN ya nemi afuwar abokan hulɗarsa kan ɗaukewar sabis a Najeriya
Karin kudin na zuwa ne sakamakon yadda Kamfanin ya sanar da cewa kudaden da ake tatsar show haraji da faduwar darajar Naira ne za su sanya ya dauke shi.
A wata kididdiga da Kamfanin ya yi ya sanar da cewa sun tafka mummunar asara sakamakon harajin Naira bilyan 137bn da suka biya.