Mijin tsohuwar Ministar Kuɗi, Kemi Adeosun ya mutu
Hausa

Mijin tsohuwar Ministar Kuɗi, Kemi Adeosun ya mutu

1786017010830
1786017010830

Anthony Adeniyi Adeosun, mijin tsohuwar Ministar Kuɗi ta Najeriya, Kemi Adeosun, ya mutu, yana da shekaru 62.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a wata sanarwa da iyalansa su ka fitar, sun bayyana cewa Anthony ya mutu a ranar Laraba, 5 ga watan Agustan 2026, a jihar Legas.

Marigayin fitaccen ɗan kasuwa ne kuma Kirista mai kishin addini, wanda aka ce ya yi rayuwa mai cike da gaskiya, hidima da kuma sadaukarwa ga iyalansa da al’ummarsa.

Iyalan marigayin sun ce za su sanar da ranar da za a gudanar da jana’iza da sauran shirye-shiryen binne shi nan gaba.

Anthony Adeosun ya bar matarsa, Kemi Adeosun, da ‘ya’yansa, da kuma ‘yan uwansa ciki har da wanda ya kafa kamfanin Kuramo Capital, Adewale Adeosun.

Iyalan sun kuma gode wa duk waɗanda suka nuna alhini tare da yi musu addu’a da ba su goyon baya a wannan lokaci na jimami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *