Kotu ta kori karar neman hana dalibai sanya hijabi
Hausa

Kotu ta kori karar neman hana dalibai sanya hijabi

Court

Kotu ta yi watsi da bukatar dakatar da dalibai Musulmi sanya hijabi a makarantar International School da ke Jami’ar Ibadan.
Karo ba biyu cikin wata shida ke nan da hukumar makarantar da ke neman hana dalibanta sanya hijabi take shan kaye a kotu a kan lamarin.

A wannan karon kotun, Mai Shari’a Moshood Isola ya yi watsi da daukaka kara da hukumar makarantar ta yi na neman dakatar da hukuncin kotun farko da ta sahale wa dalibai Musulmi sanya hijabi.

Da farko, a watan Mayu Babbar Kotun Jihar Oyo ta sahale wa daliban sanya hijabi a matsayin wani bangare na kayan makaransu.
Iyayen daliban sun yi nasara a kotu ne bayan karar da suka shigar cewa makarantar na hana daliban sanya hijabi, wanda hakkinsu da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su a matsayinsu na Musulmi.

Da yake magana kan huukuncin, shugaban kungiyar iyayen daliban, Abdur-Rahman Balogun, ya yi maraba da hakan.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *