Kotu ta ba da belin ƙananan yara da gwamnatin Najeriya ta gurfanar kan zanga-zanga
Hausa

Kotu ta ba da belin ƙananan yara da gwamnatin Najeriya ta gurfanar kan zanga-zanga

Najeriya

Babbar kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da belin mutum 67 cikin 76 da gwamnatin ƙasar ta zarga da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zangar da suka gudanar a watan Agusta.

Kotun ƙarƙashin Mai Shari’a Obiora Egwuatu ta saka wa kowannensu sharaɗin naira miliyan 10, da kuma gabatar da mutumin da zai tsaya wa kowa, wanda ta ce dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnati mai matakin albashi na 15.

Karanta Karin Wani Labarin: Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ke shirin kai hari ga masu gyaran layin lantarkin Arewa

Sai dai mutum 27 cikin waɗanda aka gurfanar a kotun ƙananan yara ne da shekarunsu ba su kai 18 ba, har da ma mai shekara 14, kamar yadda BBC ta gani a takardun kotun.

An tura manyan cikinsu zuwa gidan yari, an kuma aika da yaran wani gidan kula da kangararrun yara har zuwa ranar 25 ga watan Janairu, inda za a ci gaba da shari’ar.

An kama waɗanda ake zargin ne a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a faɗin Najeriya tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

Karanta Karin Wani Labarin: Kungiyar likitoci ta baiwa gwamnan Kano awanni 48 ya kori Kwamishiniyar sa

An kama su ne a garuruwan Kano, da Katsina, da Gombe, da Abuja, da Jos, da Kaduna.

Ana tsaka da sauraron ƙarar ne kuma yara huɗu daga cikin waɗanda ake zargin suka yanke jiki suka faɗi, abin da ya sa dole alƙalin ta dakata domin a duba su.

Daga nan sai aka fara kiran su ɗaya bayan ɗaya ana karanta musu laifukan da ake zargin su da aikatawa cikin harshen Ingilishi, inda tafinta ke fassara musu da Hausa.

Sai dai sun musanta aikata laifukan.

Karinta Karin Wani Labarin: Shugaba Tinubu Zai rantsar da sabbin Ministoci 7 ranar litinin

Wasu masu fafutika da suka zanta da BBC a harabar kotun sun ce an tsare wasu daga cikin yaran tun daga watan Agusta – kwana 80 kenan.

Daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi musu akwai cewa “sanyawa tare da ɗaga tutar Rasha, suna rera waƙoƙin juyin juya-hali tare da kira ga Rasha ta kawo ɗauki a Najeriya”.

A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da mutum 10 a gaban kotu, waɗanda ta zarga da jagorantar zanga-zangar. Daga baya kotun ta ba da belinsu kan naira miliyan 10 kowannensu, yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar tasu.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *