Majalisar zartaswa ta tarayya da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Laraba ta amince da dakatar da kafa sabbin manyan makarantu na tarayya na tsawon shekaru biyar a fadin kasar nan.
Dakatarwar ta shafi jami’o’i, polytechnics, da kwalejojin ilimi.
Tunji Alausa, ministan ilimi, ya bayyana yanayi da wajibcin dakatarwar, inda ya bayyana cewa kalubalen da ake fuskanta a fannin ilimin Najeriya a yanzu bai shafi samun damar shiga manyan makarantun tarayya ba, sai dai a magance matsalar yawan makarantun wanda ya haifar da tabarbarewar ababen more rayuwa da ma’aikata.