Gwamnan Jihar Katsina Ya Bawa Mai Digirin Da Yake Siyar Da Ruwa A Kan Titi Aiki
Hausa

Gwamnan Jihar Katsina Ya Bawa Mai Digirin Da Yake Siyar Da Ruwa A Kan Titi Aiki

Governor Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayar da aikin yi kai tsaye ga wani dalibi da ya kammala digiri mai daraja ta farko a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Sham’unu Ishaq, wanda ke sayar da ruwa a kan titi domin ciyar da iyalinsa.

Kamar yadda wani babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na zamani, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Juma’a, ya bayyana cewa #Miqdad_Jnr, gwamnan bayan lura da halin da Ishaq ke ciki, ya umarci mataimakinsa na musamman kan harkokin dalibai da ya tabbatar da ikirarin kamar yadda aka nuna a wani hoto na bidiyo.

Sanarwar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ibrahim Mohammed ya fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa mataimakin shugaban hukumar ne ya tabbatar da ikirarin Ishaq.
Sanarwar ta ce, “Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ba Sham’unu Ishaq, wanda ya kammala digiri na farko a jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua aikin yi cikin gaggawa, wanda aka gano yana sayar da pure water don tallafa wa iyalinsa.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *