Gwamna Babagana Zulum na Borno ya amince da mayar da ma’aikatan lafiya 23 da aka dakatar da su bakin aikinsu a babban asibitin Gwoza.
Zulum ya amince da hakan ne a ranar Talata a lokacin da yake duba sabuwar cibiyar kula da haihuwa da kananan yara da asibitin da aka gyara da sauran ayyukan da ake gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa tun farko an dakatar da ma’aikatan ne bayan da gwamnan ya same su basa nan a ziyarar da ya kai a baya.
“An yi koke-koke game da ma’aikatan lafiya 23 da ba su nan a ziyarar ta ta karshe.
“Dan adama tara yake, bai cika goma ba, don haka gwamnati ta yafe musu, duk da cewa ba za a biya su albashin baya ba”.