An yanke wa ɗan TikTok ɗaurin shekara 32 a gidan yari
Hausa

An yanke wa ɗan TikTok ɗaurin shekara 32 a gidan yari

1732011109011

Wani matashi ɗan shekara 21 ya zama ɗan TikTok na baya bayan nan da aka tura gidan yari a Uganda bayan ya wallafa wani bidiyo da aka ce yana cin mutuncin shugaba Yoweri Museveni.

Emmanuel Nabugodi ya bayyana ne a gaban kotu a ranar litinin bayan ya amsa laifinsa a makon da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da kalaman nuna ƙiyayya da yaɗa munanan bayanai game da shugaban ƙasar.

An yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 32 a gidan yari.

Nabugodi, wanda ya shahara wajen wallafa abubuwan barkwanci ga mabiyansa 20,000, ya yi bidiyo na wani shari’ar izgili da ake yi wa shugaban ƙasa. A ciki ya yi kira da a yi wa Museveni bulala a bainar jama’a.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun yi ta korafin yadda ake tauye ƴancin faɗin albarkacin baki a ƙasar, suna masu zargin cewa shugaban – wanda ke kan karagar mulki tun 1986 – ba ya lamuntar suka a gare shi.

A watan Yuli, an yankewa Edward Awebwa hukuncin shekaru shida akan irin wannan tuhuma da aka yi wa Nabugodi. Wasu uku kuma suna jiran hukunci kan abubuwan da suka wallafa a shafukan sada zumunta sada zumunta.

A lokacin da take zartar da hukuncin Nabugodi, Stellah Maris Amabilis, babbar alƙaliyar kotun Entebbe, ta ce bai yi nadama ba, kuma hukuncin zai taimaka wajen daƙile sukar da ake kai wa miutane a shafukan sada zumunta ciki har da na shugaban ƙasa.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *