Gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ake sa ran za a yi a Gombe ta sanar da sabuwar ranar da za ta fara gasar daga ranar 11 zuwa 16 ga Nuwamba, 2024. Babban filin wasa na Pantami zai karbi bakuncin makarantun sakandare sama da 85 daga kananan hukumomi 11 da ke fadin jihar Gombe. wanda ke nuna gagarumin ci gaba a tarihin wasanni na jihar.
Karanta Karin Wani Labarin: Majalisar dattijai ta dage zaman tantance sababbin ministoci
Tun da farko an shirya gudanar da taron a ranar 18 zuwa 24 ga Oktoba, 2024, an dage taron ne saboda wani aikin gwamnati da ya shafi ma’aikatar ilimi ta jihar. A shirye-shiryen gasar, an riga an horar da sama da Masu bada horo 65 daga makarantun sakandare daban daban, inda ake sa ran matasa ’yan wasa kusan 3,065 za su halarci wannan gasar ta firamare. inda ‘yan wasa za su yi zango a girls village lokacin gasar, an kammala, kuma ana gudanar da zaman horo a makarantu a duk fadin.
Hon. Ahmad Shu’aibu Gara-Gombe, shugaban kwamitin shirya gasar, ya bukaci shugabannin makarantu, ‘yan wasa, da masu ruwa da tsaki su shirya dalibansu domin wannan gagarumin gasar .
Ya kuma jaddada cewa, duk shirye shiryen gudanar da gasar suna cikin tsari, kuma karin lokacin da aka samu daga gyare gyaren jadawalin zai ba da damar masu daukar nauyin kulla kawancen da za su kara habaka gasar wasannin motsa jiki, wanda kuma za a rika yadawa ta yanar gizo ga masu sauraro a duniya.
Karanta Karin Wani Labarin: BIDIYO: Yan jarida na da rawar da zasu taka wajan hada kan kasashen Afrika – Hajiya Maryam
Shugaban na Green White Green (GWG) Sports Center Ltd, Hon. Gombe, ya nuna jin dadinsa kan yadda aka daidaita wannan sabuwar ranar tare da masu ruwa da tsaki daga ma’aikatun wasanni da ilimi. Ya kuma jaddada kudirinsa na ganin cewa gasar wasannin guje guje da tsalle tsalle ta tsakanin makarantun gaba da sakandire ta Gombe ta zama abin tunawa, wanda ya zaburar da sauran jihohin kasar nan wajen yin koyi da shi.
Sanarwar sabuwar ranar ta sake farfado da sha’awa a tsakanin makarantun da ke halartar gasar, tare da yin kokarin ba da horo mai zurfi a shirye shiryen gasar.