Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 16, ta lalata gidaje 3,936 a Jigawa
Hausa

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 16, ta lalata gidaje 3,936 a Jigawa

mutane

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), ta tabbatar da mutuwar mutane 16 tare da lalata gidaje 3,936 sakamakon ambaliyar ruwa.

Ya kuma ce ambaliya ta kuma mamaye kadada 2,744 na gonaki biyo bayan mamakon ruwan sama tun da aka fara daminar shekarar 2024.

Karin Wani Labarin: Rundunar Sojin Najeriya ta gano wurin ƙera makamai a Plateau

Sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Haruna Mariga, wanda ya bayyana hakan a Dutse ranar Laraba, ya ce bala’in ya shafi kananan hukumomi 10 na jihar.

Mairiga ya ce mutanen sun mutu ne sakamakon rugujewar gine-gine, nutsewa da kwalekwale.

Karin Wani Labarin: Ƴan mata uku sun mutu a ruwa yayin zuwa yanko ciyawa a Jigawa

Ya ce bala’in ya yi sanadin mutuwar mutane 16 tare da mutane 3,936 da suka rasa matsugunansu yayin da hekta 2,744 na gonaki suka nutse,” in ji shi.

Ya kara da cewa lamarin na iya kara kamari saboda yawan ruwan sama da ake sa ran zai yi.
Mairiga ya ce hukumar ta samar da matsuguni na wucin gadi tare da raba kayan agaji ga ‘yan gudun hijirar domin rage musu radadi. Kayayyakin da suka hada da shinkafa, masara, gyadar masara, barguna, taliya, da tabarmi.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *