Aƙalla mayaƙa 400 ne suka miƙa wuya a Nijar
Hausa

Aƙalla mayaƙa 400 ne suka miƙa wuya a Nijar

NGR, mayaƙa

Akalla sama da mayaƙa 400 da suke addabar yankunan arewacin jamhuriyar Nijar ne suka miƙa wuya a birnin Agadez, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar, ANP ta ruwaito.

Rahoton ya ƙara da cewa mayaƙan ƴan ƙungiyar Patriotic Liberation Front da Movement for Justice and Rehabilitation of Niger ne.

Karanta Karin Wani Labarin: Rundunar Sojojin Najeriya ta kama wani dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Habu Dogo

An ce mayaƙan sun amince da kiran shugaban ƙasa Janar Abdourahmane Tchiani na miƙa wuya ne.

Ba a taɓa samun mayaƙa da suka kai wannan adadin ba, sannan a ranar 3 da 11 ga watan Nuwamba ma an samu irin hakan, inda wasu mayaƙan daban suka miƙa wuya a birnin na Agadez.

Mayaƙan suna faɗa ne tare da kira da a saki shugaban ƙasa Mohamed Bazoum da aka hamɓarar.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *