Daga Zulaiha Danjuma
Iƙirari
Shin Gwamnatin Tarayya Na Raba Tallafin ₦50,000 Ga Duk Wanda Ya Tura Sakon ‘YES’ Zuwa Lambar 2684?
Wani sako da ke yawo cikin gaggawa a kafafen sada zumunta, musamman a WhatsApp, na Iƙirari cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya na raba tallafin kudi naira ₦50,000. Sakon yana umartar yan kasa da su tura kalmar “YES” zuwa gajeren lambar nan 2684 domin su sami wannan tallafi kyauta.
Sakamakon Bincike
KARYA NE. Ko da yake gajeren lambar nan 2684 ta hukumar gwamnati ce, da’awar da ke yawo cewa kowa zai iya tura sako zuwa lambar domin samun ₦50,000 ta atomatik ƙarya ce gaba ɗaya. Wannan sako yaudara ce ta intanet wadda ke jefa mutane cikin haɗarin faɗawa hannun yan damfara masu satar bayanan sirri na banki.
Cikakken Bayani da Abubuwan da Aka Gano:
1. Asalin Lambar:
Gajeren lambar nan 2684 na wani shiri ne na hukumar gwamnatin tarayya, wato National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI), wanda Ma’aikatar Agaji da Rage Raɗadin Talauci ta Tarayya ke gudanarwa.
2. Yadda Ainihin Shirin Ke Aiki:
Bayanai daga jagororin shirin na hukuma da rahotannin kafafen yaɗada labarai da suka haɗa da jaridar The Punch sun nuna cewa wannan lamba ba dandalin neman tallafi ba ne ga kowa da kowa. Shirin yana aiki ne kawai ga mutanen da aka riga aka zaɓa (pre-selected), inda ake amfani da gajeren lambar domin tattaunawa kawai da gidaje masu ƙaramin ƙarfi waɗanda sunansu ya riga ya shiga cikin Rajistan Tallafi ga marasa ƙarfi da gajiyayyu na Ƙasa (National Social Register).
Maimakon ta zama hanyar neman tallafi, lambar a gaske hanya ce ta bayyana amincewa (consent tool). Gwamnati ce ke aiko da sako (SMS) daga lambar 2684 zuwa ga waɗannan zaɓabbun mutane. Mayar da martani da kalmar “YES” yana ba gwamnati damar amincewa ne kawai ta saka kuɗan tallafin a asusunsu na tafi-da-gidanka (mobile wallets). Wannan tsari ba buɗe rajista ba ne ga kowa. Sakonnin da mutanen da ba a zaɓa ba suka tura wa 2684 ba za su ba su damar samun tallafin ₦50,000 ba.
Sai dai kuma, akwai wata dabarar amsawa ta atomatik daga kamfanonin sadarwa. Idan mutanan da ba a zaɓa ba ya tura “YES” zuwa 2684, tsarin kwamfuta na kamfanonin sadarwar zai turo masa da bayanan yadda zai buɗe asusun tafi-da-gidanka (kamar MTN MoMo, Wema ALAT, ko OPay). Yan damfara da mutanen da ba su da cikakken bayani sai su ɗauki hoton wannan amsa (screenshot) su rarraba a matsayin “hujja” cewa tsarin yana aiki.
A gaskiya, tsarin kawai yana nuna wa mutum yadda zai buɗe daidaitaccen asusun banki ne na tafi-da-gidanka wanda babu ko kwabo a ciki. Babu kuɗaɗen gwamnati da ke maƙale da shi.
3. Haɗuran tsaron dangane da Intanet (Cybersecurity Risk)
Kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet (kamar OPay) da masana harkar tsaro sun fitar da gargaɗi game da wannan ɗabi’a. Yan damfara suna amfani da wannan saƙon da ke yawo domin farautar mutane. Da zarar mutum ya tura saƙo zuwa lambar ko ya buɗe asusu, ‘an damfara na iya kiransa ko su tura masa saƙo suna riya cewa su “ma’aikatan gwamnati ne” domin su sace lambobin BVN, NIN, ko lambar sirri (PIN) ta asusunsa.
Kammalawa
Kada ka tura “YES” zuwa lambar 2684 face idan gwamnati ce da kanta ta fara aiko maka da saƙo kai tsaye. Kuma hakan zai faru ne kawai idan an riga an yi wa gidanku rajista a Rajistan Tallafi ga marasa ƙarfi da gajiyayyu na Ƙasa (NSR) wanda hukumar NASSCO ke kula da shi.
