Shugaba Bola Tinubu a daren Juma’a ya isa birnin Rio de Janeiro na Brazil, domin halartar taron BRICS karo na 17.
Wannan shi ne karon farko da Najeriya ta kara kulla kwance da BRICS.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar My Bayo Onanuga ya fitar, jirgin saman shugaban kasar da ya taso daga Saint Lucia a safiyar yau, ya isa sansanin sojin sama na Galeao da misalin karfe 8:45 na dare.