Yan Majalisar Wakilai Hudu Na Labour Party Sun Fice Daga Jam’iyyar 
Hausa

Yan Majalisar Wakilai Hudu Na Labour Party Sun Fice Daga Jam’iyyar 

Reps 750x430.jpeg

Yan majalisar wakilai hudu sun sauya sheka daga jam’iyyar Labour Party (LP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya sanar da sauya shekar ‘yan majalisar a zauren zauren majalisar a ranar Alhamis.

‘Yan majalisar sun hada da Chinedu Okere (Mazabar Owerri/Owerri North/Owerri west federal constituency), Mathew Donatus (Kaura federal constituency of Kaduna), Akiba Bassey (Calabar municipal/Odukpani federal constituency of Cross River), da Esosa Iyawe (Oredo federal constituency of Edo).
‘Yan majalisar dai sun danganta sauya shekar nasu da rikicin da ake zargin jam’iyyar LP ta samu.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *