Rahotanni daga jihar Neja na cewa a yanzu haka ƴan bindiga da dama na zaune a cikin gidajen al’ummar garin Alawa , kuma suna noma a gonakinsu tare da yin amfani da takin zamanin da su ka bari a gidajensu.
Watanni biyar ke nan da su ka gabata ƴan bindigar suka fatattaki mazauna garin na Alawa tare da korar su daga matsuguninsu kuma suka mayar da su ƴan gudun hijira.
Karin Wani Labarin: ’Yan bindiga sun kashe matafiya 7 a hanyar Taraba
Wani mazaunin garin wanda ke gudun hijira ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne bayan da gwamnati ta janye jami’an tsaron da ke ba su kariya domin a cewar gwamnatin tana so ta canza tsari, “sai dai har yanzu ba a mayar da sojojin ba.”
“Wasu daga cikin mu sun yi ƙundunbala, kasancewar halin matsi, sun yi ƙoƙarin leƙawa domin su ganin ko za mu iya komowa, sai dai sun iske abun mamaki, an ƙoƙƙona gidajenmu, sun kuma kwashe takin da muka baro suna amfani da shi a yankin Alawa, yanzu haka ɓarayin suna noma a dajin Alawa.”
Karin Wani Labarin: Shugaban karamar da akai garkuwa dashi a Kogi ya tsere daga hannun masu garkuwan – Yan sanda
Jihar Neja, musamman yankunanta da ke kan iyaka da jihar Kaduna da Kebbi na fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Gwamnatin tarayya da ta jihar sun sha nanata cewa suna ƙoƙarin wajen ganin sun shawo kan matsalar sai dai har yanzu ƴan bindigar na ci gaba da kai hare-hare kan al’umma.
Mutumin da muka sakaya sunansa, ya ce ba su taɓa tunanin haka za ta faru ba, “kasancewar gwamnati, ta yi mana alƙawarin za ta yi abun da yakamata, amman har yanzu ba ta yi abun da ya dace ba.
Ya kuma shaida wa BBC cewa suna fatan sake komawa garin nasu, “maganar komawa akwai ta, in har gwamnati za ta tallafa mana.”
Sai dai gwamnatin jihar Neja ta musanta wannan iƙirari na zaman ƴan bindiga cikin garin Alawa.
“Kwamishinan tsaro na jihar Neja, Bello Muhammad ya ce gaskiya ne mutanen ba sa gidajensu, sai dai ba gaskiya ba ne cewa ƴan bindiga suna gidajensu suna kuma noma a wajen.
Karin Wani Labarin: Ƴan mata uku sun mutu a ruwa yayin zuwa yanko ciyawa a Jigawa
“Idan suna noma a wajen ai kama su za mu je mu yi, koda sojoji ba su wurin amman ana rangadi har ta sama kowane lokaci, ba mu da sansanin ƴan bindiga a jiharmu,” cewar kwamishinan.
Gwamnatin ta jihar Neja ta ce tana nema wa mutanen wurin da za su koma domin su ci gaba da yin rayuwa tare da yin noma a wasu wuraren.
Matsalar rashin tsaro a yankunan karkara ta tarwatsa mutane da dama, inda hakan ya haifar da raguwa sosai na ayyukan gona, lamarin da ke barazana ga wadatar abinci a Najeriya.
Sai dai baya ga fararen hula, ƴan bindigar kan kai hare-hare kan jami’an tsaro.
Shekara ɗaya da ta gabata, irin waɗannan ƴan bindiga sun yi wa sojoji kwanton-ɓauna inda suka harbo jirgi mai saukar ungulu da ke ɗauke da wasu sojojin da ke aiki a yankin Zungeru na jihar ta Neja.
Lamarin ya haifar da asarar aƙalla sojoji 36, kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta sanar.