Jam’iyyar NNPP ta ce dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sen. Rabiu Kwankwaso, ba shi da damar yin takara da shugaba Bola Tinubu da ko wani dan takarar shugaban kasa a halin yanzu a 2027.
Shugaban NNPP na kasa, Dr Agbo Major ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Major yana magana ne a kan maganar da Buba Galadima ya yi na cewa Kwankwaso zai tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP.
Agbo ya bayyana cewa, tuni jam’iyyar NNPP ta kore da Kwankwaso da Galadima, saboda kama su da yiwa jam’iyyar zagon kasa.